Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 99 (Sura 99)
1; Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
2; Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
3; Kuma mutum ya ce “Mħ neya same ta?”
4; A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
5; cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
6; A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
7; To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
8; Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.

Pages ( 99 of 114 ): « Previous1 ... 9798 99 100101 ... 114Next »