Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 88 (Sura 88)
1; Lalle ne labãrin (Ƙiyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
2; Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
3; Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
4; Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
5; Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
6; Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
7; Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
8; Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni´ima ne.
9; Game da aikinsu, masu yarda ne.
10; (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
11; Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
12; A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
13; A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
14; Da kõfuna ar´aje.
15; Da filõli(3) jħre,
16; Da katifu shimfiɗe.
17; Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
18; Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
19; Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
20; Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
21; sabõda haka, ka yi wa´azi, kai mai yin wa´azi ne kawai.
22; Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
23; Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
24; To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
25; Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
26; Sa´an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.

Pages ( 88 of 114 ): « Previous1 ... 8687 88 8990 ... 114Next »