Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 83 (Sura 83)
1; Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
2; Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
3; Kuma idan sun auna musu da zakka(1) ko da sikħli, suna ragħwa
4; Ashe! Waɗancan bã su tabbata cħwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
5; Domin yini mai girma.
6; Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
7; Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
8; Kuma, mħ ya sanar da kai abin da akħ cħ wa Sijjĩn?
9; Wani 1ittãfi ne rubũtacce.
10; Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
11; Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
12; Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙħtare haddi mai yawan zunubi.
13; Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
14; A´aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
15; A´aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancħwa ne.
16; Sa´an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
17; Sa´an nan a ce: “Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi.”
18; A´aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã´ã yana a cikin Illiyyĩna?
19; Kuma mħne ne yã sanar da kai abin da ake cħwa Illiyyũna?
20; Wani littãfi ne rubũtacce.
21; Muƙarrabai(1) suke halarta shi.
22; Lalle ne, mãsu ɗã´ã ga Allah tabbas suna cikin ni´ima.
23; A kan karagu, suna ta kallo.
24; Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni´ima.
25; Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
26; Ƙarshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nħma.
27; Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
28; (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
29; Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
30; Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
31; Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
32; Kuma idan sun gan su sai su ce: “Lalle waɗannan ɓatattu ne.”
33; Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
34; To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni,sũ ke yi wa kãfirai dãriya
35; A kan karagu, suna ta kallo.
36; Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?(1)

Pages ( 83 of 114 ): « Previous1 ... 8182 83 8485 ... 114Next »