Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 80 (Sura 80)
1; Yã game huska(1) kuma ya jũya bãya.
2; Sabõda makãho yã je masa.
3; To, me ya sanar da kai cħwa watakila shi ne zai tsarkaka.
4; Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
5; Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
6; Sa´an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
7; To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
8; Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
9; Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
10; Kai kuma kã shagala ga barinsa!
11; A´aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
12; Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
13; (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
14; Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakħwa.
15; A cikin hannãyen mala´iku marubũta.
16; Mãsu daraja, mãsu ɗã´a ga Allah.
17; An la´ani mutum (kafiri). Mħ yã yi kãfircinsa!
18; Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
19; Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa´an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
20; Sa´an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
21; Sa´an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
22; Sa´an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
23; Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
24; To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
25; Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
26; Sa´an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
27; Sa´an nan, Muka tsirar da ƙwaya ,a cikinta.
28; Da inabi da ciyãwa.
29; Da zaitũni da itãcen dabĩno.
30; Da lambuna, mãsu yawan itãce.
31; Da ´yã´yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
32; Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
33; To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
34; Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan´uwansa.
35; Da uwarsa da ubansa.
36; Da mãtarsa da ɗiyansa.
37; Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha´ani da ya ishe shi.
38; Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
39; Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
40; Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
41; Baƙi zai rufe su.
42; Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).

Pages ( 80 of 114 ): « Previous1 ... 7879 80 8182 ... 114Next »