Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 44 (Sura 44)
1; Ḥ. M̃.
2; Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
3; Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ´ Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
4; A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
5; Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
6; Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
7; (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).
8; Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashħwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
9; A´a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
10; Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
11; Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
12; Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
13; Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?
14; Sa´an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: “Wanda ake gayãwa(1) ne, mahaukaci.”
15; Lalle Mũ, Mãsu kuranyħwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).
16; Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
17; Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir´auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jħ musu.
18; (Mazon ya ce): “Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku.”
19; “Kuma kada ku nħmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne.”
20; “Kuma lalle nĩ na nħmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jħfe ni.”
21; “Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni.”
22; Sai ya kirayi Ubangjinsa cħwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
23; (Allah Ya ce): “To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)”
24; “Kuma ka bar tħku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa.”
25; Da yawa suka bar gõnaki da marħmari.
26; Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.
27; Da wata ni´ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
28; Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
29; Sa´an nan samã da ƙasã ba su yi kũka(1) a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
30; Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã´ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
31; Daga Fir´auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.
32; Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.
33; Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu´ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni´ima bayyananna(2)
34; Lalle waɗannan mutãne(3) , haƙĩka, sunã cħwa,
35; “Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba.”
36; “Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya.”
37; shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba´u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.
38; Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.
39; Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.
40; Lalle rãnar rarrabħwa, ita ce lõkacin wa´adinsu gabã ɗaya.
41; Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.
42; fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
43; Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),
44; Ita ce abincin mai laifi.
45; Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.
46; Kamar tafasar ruwan zãfi.
47; (A cħ wa malã´ikun wutã), “Ku kãmã shi, sa´an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm.”
48; “Sa´an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi.”
49; (A ce masã), “Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!”
50; “Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi.”
51; Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.
52; A cikin gidãjen Aljanna da marħmari.
53; Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.
54; Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.
55; Sunã kira, a cikinsu (gidħjen) ga dukan ´ya´yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).
56; Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.
57; Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
58; Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur´ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.
59; Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.(1)

Pages ( 44 of 114 ): « Previous1 ... 4243 44 4546 ... 114Next »