Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 100 (Sura 100)
1; Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
2; Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
3; Sa´an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
4; Sai su motsar da ƙũra game da shi.
5; Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama´ar maƙiya.
6; Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
7; Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
8; Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
9; Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
10; Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
11; Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Pages ( 100 of 114 ): « Previous1 ... 9899 100 101102 ... 114Next »