Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 56 (Sura 56)
1; Idan mai aukuwa ta auku.
2; Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
3; (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
4; Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
5; Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙħwa.
6; Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
7; Kuma kun kasance nau´i uku.
8; Watau mazõwa dãma.(1) Mħne ne mazõwa dãma?
9; Da mazõwa hagu. Mħne ne mazõwa hagu?
10; Da waɗanda suka tsħre.Sũ wɗanda suka tsħren nan,
11; Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
12; A ckin Aljannar ni´ima.
13; Jama´a ne daga mutãnen farko.(2)
14; Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
15; (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
16; Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
17; Wasu yara samãri na dindindin għwaya a kansu.
18; Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
19; Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
20; Da wasu ´ya´yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
21; Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha´awa.
22; Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
23; Kamar misãlan lu´ulu´u wanda aka ɓõye.
24; A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
25; Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
26; Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
27; Da mazõwa dãma. Mħne ne mazõwa dãma?
28; (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
29; Da wata ayaba mai yawan ´ya´ya.
30; Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
31; Da wani ruwa mai gudãna.
32; Da wasu ´ya´yan itacen marmari mãsu yawa.
33; Bã su yankħwa kuma bã a hana su.
34; Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
35; Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
36; Sa´an nan Muka sanya su budurwai.
37; Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
38; Ga mazõwa dãma.
39; Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
40; Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
41; Mazõwa hagu, Mħne ne mazõwa hagu?
42; Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
43; Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
44; Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni´ima ba.
45; Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
46; Kuma sun kasance sunã dõgħwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
47; Kuma sun kasance sunã cħwa: “Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?”
48; “Shin, kuma da ubanninmu na farko?”
49; Ka ce: “Lalle mutãnen farko da na ƙarshe.”
50; “Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne.”
51; “Sa´an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!”
52; “Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã).”
53; “Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta.”
54; “Sa´an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi.”
55; “Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa.”
56; Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
57; Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
58; Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
59; Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
60; Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa(1) ba,
61; A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
62; Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
63; Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
64; Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
65; Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa,sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
66; (Kunã cħwa) “Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!”
67; “ôa, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!”
68; Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
69; Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
70; Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdħwa?
71; Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
72; Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
73; Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa´azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jħji.
74; Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
75; To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
76; Kuma lalle ne´ haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
77; Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
78; A cikin wani littafi tsararre.
79; Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
80; Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
81; Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
82; Kuma kunã sanya arzikinku ( game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
83; To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
84; Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
85; Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
86; To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
87; Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya(1) .
88; To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
89; Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni´ima.
90; Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
91; Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
92; Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
93; Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
94; Da ƙõnuwa da Jahĩm,
95; Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
96; Sabõda haka, ka tsarkake(2) sũnan Ubangijinka, Mai karimci.

Pages ( 56 of 114 ): « Previous1 ... 5455 56 5758 ... 114Next »