Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 89 (Sura 89)
1; Inã rantsuwa da alfijiri.
2; Da darũruwa gõma.
3; Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.
4; Da dare idan yana shũɗewa.
5; Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?
6; Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?
7; Iramawa mãsu sakon(1) ƙĩrar jiki.
8; Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).
9; Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi(2) suka yi gidãje)?
10; Da Fir´auna mai turãku.
11; Waɗanda suka ƙħtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?
12; Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.
13; Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.
14; Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.
15; To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni´ima, sai ya ce: “Ubangijina Ya girmama ni.”
16; Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: “Ubangijina Ya walãkanta ni.”
17; A´aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!
18; Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!
19; Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.
20; Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.
21; A´aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.
22; Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã´iku na jħre, safũ- safu.
23; Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!
24; Yana dinga cħwa, “Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!”
25; To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.
26; Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.
27; Yã kai rai mai natsuwa!
28; Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).
29; Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya).
30; Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).

Pages ( 89 of 114 ): « Previous1 ... 8788 89 9091 ... 114Next »