Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 113 (Sura 113)
1; Ka ce “ina neman tsari ga Ubangijin safiya”
2; “Daga sharrin abin da Ya halitta.”
3; “Da sharrin dare, idan ya yi duhu.”
4; “Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle-ƙulle.”
5; “Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada.”

Pages ( 113 of 114 ): « Previous1 ... 111112 113 114Next »