Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 50 (Sura 50)
1; Ƙ̃ . Inã rantsuwa da Alƙur´ãni Mai girma.
2; ôa, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: “Wannan wani abu ne mai ban mãmãki.”
3; “Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa.”
4; Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragħwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarħwa.
5; ôa, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al´amari mai raurawa.
6; Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
7; Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jħfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma´auri mai ban sha´awa?
8; Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
9; Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa´an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbħwa.
10; Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da´ya´yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
11; Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
12; Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma´abũta Rassi,(1) da Samũdãwa.
13; Da Ãdãwa da Fir´auna da ´yan´uwan Lũɗu.
14; Da ma´abũta ƙunci(2) da mutãnen Tubba´u,(3) kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacħwaTa ta tabbata.
15; Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? ôa, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
16; Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayħnsa.
17; A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã´ika) zaunanne.
18; Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
19; Kuma mãyen mutuwa ya jħ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirħwa.
20; Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacħwar ne fa.
21; Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
22; (Sai a ce masa): “Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne.”
23; Kuma abõkin haɗinsa(1) ya ce: “Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce.”
24; (A ce wa Malã´iku), “Ku jħfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai.”
25; “Mai yawan hanãwa ga alhħri, mai zãlunci, mai shakka.”
26; “Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujħfa shi a cikin azãba mai tsanani.”
27; Abõkin haɗinsa(2) ya ce: “Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa.”
28; Ya ce: “Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku.”
29; “Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa.”
30; Rãnar da Muke cħwa ga Jahannama “Shin, kin cika?” Kuma ta ce: “Ashe,(3) akwai wani ƙãri?”
31; Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
32; “Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa´adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
33; “Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake,(4) kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali.”
34; (A ce musu) “Ku shige ta da aminci,(5) waccan ita ce rãnar dawwama.”
35; Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni´ima,
36; Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al´ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa´an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: ´Kõ akwai wurin tsĩra´?(1) ( Babu).
37; Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jħfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
38; Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata´yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
39; Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi(2) game da gõdħ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacħwarta.
40; Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
41; Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri(3) makusanci.
42; Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
43; Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashħwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
44; Rãnar da ƙasã ke tsattsãgħwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
45; Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur´ani,(4) ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.

Pages ( 50 of 114 ): « Previous1 ... 4849 50 5152 ... 114Next »