Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 54 (Sura 54)
1; Sã´a ta yi kusa, kuma wata(7) ya tsãge.
2; Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: “Sihiri ne mai dõgħwa!”
3; Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al´amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
4; Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
5; Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
6; Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
7; Ƙasƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
8; Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cħwa, “Wannan yini ne mai wuya!”
9; Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: “Shi mahaukaci ne.” Kuma aka tsãwace shi.
10; Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), “Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako.”
11; Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
12; Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
13; Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
14; Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
15; Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
16; To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
17; Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur´ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
18; Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
19; Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgħwa.
20; Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
21; To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
22; Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur´ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
23; Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
24; Sai suka ce: “Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.
25; “Shin, an jħfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? ôa, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!”
26; Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
27; Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar(1) ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
28; Kuma ka bã su lãbãri cħwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.
29; Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa´an nan ya sõke ta,
30; To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
31; Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
32; Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur´ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
33; Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
34; Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.
35; Sabõda wata ni´ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
36; Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
37; Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nħme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. “To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa.”
38; Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
39; To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
40; Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur,ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
41; Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jħ wa mabiyan Fir´auna.
42; Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
43; Shin, kãfiranku ne mafi alhħri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã´a a cikin littattafai?
44; Kõ zã su ce: “Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?”
45; Zã a karya(1) tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
46; ôa, Sã´a ita cħ lõkacin wa´adinsu, kuma Sã´ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
47; Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
48; Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. “Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar.”
49; Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
50; Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
51; Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
52; Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
53; Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
54; Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
55; A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.

Pages ( 54 of 114 ): « Previous1 ... 5253 54 5556 ... 114Next »