Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 111 (Sura 111)
1; Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
2; Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
3; Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
4; Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).(2)
5; A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar Ƙiyãma).

Pages ( 111 of 114 ): « Previous1 ... 109110 111 112113114Next »