Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 102 (Sura 102)
1; Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
2; Har kuka ziyarci kaburbura.
3; A´aha! (Nan gaba) zã ku sani.
4; Sa´an nan, tabbas, zã ku sani.
5; Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
6; Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
7; Sa´an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
8; Sa´an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni´imar (da aka yi muku).

Pages ( 102 of 114 ): « Previous1 ... 100101 102 103104 ... 114Next »