Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 82 (Sura 82)
1; Idan sama ta tsãge.
2; Kuma idan taurãri suka wãtse.
3; Kuma idan tħkuna aka facce su.
4; Kuma idan kaburbura aka tõne su.
5; Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
6; Yã kai mutum! Mħ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
7; Wanda Ya halitta ka sa´an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
8; A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
9; A´aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
10; Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
11; Mãsu daraja, marubũta.
12; Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
13; Lalle ne, mãsu ɗã´ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni´ima.
14; Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
15; Zã su shigħ ta a rãnar sakamako.
16; Bã zã su faku daga gare ta ba.
17; Kuma mħ ya sanar da kai abin da ake cħ wa rħnar sakamako?
18; Sa´an nan, mħ ya sanar da kai abin da ake cħ wa rãnar sakamako?
19; Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al´amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

Pages ( 82 of 114 ): « Previous1 ... 8081 82 8384 ... 114Next »