Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 78 (Sura 78)
1; A kan mħ suke tambayar jũna?
2; A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur´ãni)?
3; Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
4; A´aha! Zã su sani.
5; Kuma, a´aha! Zã su sani.
6; Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
7; Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
8; Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
9; Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
10; Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
11; Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nħman abinci?
12; Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
13; Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
14; Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
15; Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
16; Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
17; Lalle ne, rãnar rarrabħwa tã kasance abin ƙayyadħ wa lõkaci.
18; Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama´a jama´a.
19; Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
20; Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
21; Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
22; Ga mãsu ƙħtare iyãkõki, tã zama makõma.
23; Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
24; Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
25; Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
26; Sakamako mai dãcħwa.
27; Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
28; Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
29; Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigħ shi, a rubũce.
30; Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
31; Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
32; Lambuna da inabõbi.
33; Da cikakkun ´yammata, tsãrar jũna.
34; Da hinjãlan giya cikakku.
35; Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
36; Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
37; Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
38; Rãnar da Rũhi da malã´iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
39; Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
40; Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: “Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!”

Pages ( 78 of 114 ): « Previous1 ... 7677 78 7980 ... 114Next »