Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 79 (Sura 79)
1; Ina rantsuwa da mala´iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
2; Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
3; Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
4; Sa´an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsħre.
5; Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
6; Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
7; Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
8; Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
9; Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
10; Sunã cħwa “Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
11; “Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?”
12; Suka ce: “Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!”
13; To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
14; Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
15; Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
16; A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
17; Ka tafi zuwa ga Fir´auna, lalle ne shi, ya ƙħtare haddi.
18; “Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.
19; “Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?”
20; Sai ya nũna masa ãyar(1) nan mafi girma.
21; Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),
22; Sa´an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
23; Sai ya yi gayya, sa´an nan ya yi kira.
24; Sai ya ce: “Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka.”
25; Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
26; Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
27; Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
28; Ya ɗaukaka rufinta, sa´an nan Ya daidaita ta.
29; Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
30; Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
31; Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
32; Da duwatsu, Yã kafe ta.
33; Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
34; To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
35; Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
36; Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
37; To, amma wanda ya yi girman kai.
38; Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).
39; To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
40; Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
41; To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
42; Sunã tambayar ka game da sa´a, wai yaushe ne matabbatarta?
43; Me ya haɗã ka da ambatonta?
44; Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al´amarinta yake.
45; Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
46; Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marħce ko hantsinsa.

Pages ( 79 of 114 ): « Previous1 ... 7778 79 8081 ... 114Next »