Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 86 (Sura 86)
1; Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
2; To, mħ yã sanar da kai abin da ake cħwa mai aukõwa da dare?
3; Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.(1)
4; Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
5; To, mutum ya dũba, daga mħ aka halittã shi?
6; An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
7; Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
8; Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
9; Rãnar da ake jarrabawar asirai.
10; Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
11; Ina rantsuwa da sama ma´abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankħwa.
12; Da ƙasa ma´abũciyar tsãgħwa,(2)
13; Lalle ne shĩ (Alƙur´ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki(3)
14; Kuma shĩ bã bananci(4) bane
15; Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
16; Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
17; Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.

Pages ( 86 of 114 ): « Previous1 ... 8485 86 8788 ... 114Next »