Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 37 (Sura 37)
1; Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
2; Sa´an nan mãsu yin tsãwa(1) dõmin gargaɗi.
3; Sa´an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
4; Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa Ɗaya ne.
5; Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
6; Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
7; Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
8; Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama´a mafi ɗaukaka (Malã´iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane għfe.
9; Dõmin tunkuɗħwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
10; Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
11; Ka tambaye su: “Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?” Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
12; ôa, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
13; Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
14; Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
15; Kuma su ce, “Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne.”
16; “Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa,ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
17; “Ashe kõ da ubanninmu na farko?”
18; Ka ce: “Na´am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu.”
19; Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
20; Kuma su ce: “Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako.”
21; Wannan ita ce rãnar rarrabħwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
22; Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
23; Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
24; Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
25; Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
26; ôa, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
27; Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
28; Suka ce: “Lalle kũ, kun kasance kunã jħ mana daga wajen dãma (inda muka amince).”
29; Suka ce: “ôa, ba ku kasance mũminai ba.
30; “Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. ôa, kun kasance mutãne ne mãsu kħtare iyãka.”
31; “Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne.”
32; “Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu.”
33; To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
34; Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
35; Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: “Bãbu abin bautãwa, fãce Allah,” sai su dõra girman kai.
36; Kuma sunã cħwa, “Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
37; ôa, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
38; Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
39; Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
40; Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
41; Waɗannan sunã da abinci sananne.
42; ´Ya´yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
43; A cikin gidãjen Aljannar ni´ima.
44; A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
45; Anã kħwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marħmari.
46; Farã mai dãɗi ga mashãyan.
47; A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
48; Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
49; Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
50; Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
51; Wani mai magana daga cikinsu ya ce: “Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya).”
52; Yanã cewa, “Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?”
53; “Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?”
54; (Mai maganar) ya ce: “Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?”
55; Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
56; Ya ce (masa), “Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni.”
57; “Kuma bã dõmin ni´imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã).”
58; “Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba.”
59; “Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?”
60; Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
61; Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
62; Shin wancan shĩ ne mafi zama alhħri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
63; Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
64; Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
65; Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
66; To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa´an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
67; Sa´an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
68; Sa´an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
69; Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
70; Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
71; Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
72; Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
73; Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
74; Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
75; Kuma lalle, haƙĩƙa´ Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
76; Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
77; Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
78; Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama´ar ƙarshe.
79; Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
80; Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
81; Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.
82; Sã´an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
83; Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
84; A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
85; A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, “Mħne ne kuke bautãwa?”
86; “Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?”
87; “To, mħne ne zatonku game da Ubangijin halittu?”
88; Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
89; Sã´an nan ya ce: “Nĩ mai rashin lãfiya ne.”
90; Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
91; Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa´an nan ya ce: “Ashe bã zã ku ci ba?
92; “Me ya sãme ku, bã ku magana?”
93; Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
94; Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
95; Ya ce, “Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
96; “Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?”
97; Suka ce: “Ku gina wani gini sabõda shi, sa´an nan ku jħfa shi a cikin Jahĩm.”
98; Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
99; Kuma (Ibrahĩm] ya ce: “Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni.”
100; “Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne.”
101; Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro(1) mai haƙuri.
102; To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: “Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mħ ka gani?” (Yãron) ya ce: “Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri.”
103; To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga għfen gõshinsa.
104; Kuma Muka kira shi cħwa “Ya Ibrahĩm!”
105; “Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin.” Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
106; Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
107; Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
108; Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
109; Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
110; Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
111; Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
112; Kuma Muka yi masa bushãra(1) Da Is´hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
113; Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is´hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
114; Kuma lalle, Mun yi ni´ima ga Mũsã da Hãrũna.
115; Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
116; Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
117; Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
118; Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
119; Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
120; Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
121; Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
122; Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai.
123; Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
124; A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, “Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?”
125; “Shin, kunã bauta wa Ba´al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?”
126; “Allah Ubangijinku,kuma Ubangijin ubanninku farko?”
127; Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
128; Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
129; Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
130; Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
131; Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
132; Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
133; Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
134; A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
135; Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
136; Sã´an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
137; Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
138; Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
139; Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
140; A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
141; Sã´an nan ya yi ƙuri´a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
142; Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
143; To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
144; Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
145; Sai Muka jħfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
146; Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
147; Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
148; Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
149; Sabõda haka, ka tambaye su, “Shin, Ubangijinka ne da ´ya´ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?”
150; Kõ kuma Mun halitta malã´iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
151; To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cħwa.
152; “Allah Yã haihu,” alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
153; Shin, Yã zãɓi ´yã´ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
154; Mħ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?
155; Shin, bã ku tunãni?
156; Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
157; To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
158; Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, “Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)”
159; Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
160; Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
161; To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
162; Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
163; Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
164; “Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,(1) fãce yanã da matsayi sananne.”
165; “Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda).”
166; “Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi.”
167; Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cħwa,
168; “Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko.”
169; “Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.”
170; Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
171; Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
172; Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
173; Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
174; Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
175; Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.(2)
176; Shin fa, da azabarMu suke nħman gaggãwa?
177; To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
178; Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
179; Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
180; Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
181; Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
182; Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.

Pages ( 37 of 114 ): « Previous1 ... 3536 37 3839 ... 114Next »