Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 69 (Sura 69)
1; Kiran gaskiya!
2; Mħne ne kiran gaskiya?
3; Kuma mħ ya sanar da kai abin da ake cħwa kiran gaskiya?
4; Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
5; To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
6; Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙħtare haddi.
7; (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
8; To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
9; Kuma Fir´auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.
10; Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).
11; Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙħtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.
12; Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).
13; To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
14; Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
15; A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
16; Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
17; Kuma malã´iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã´iku) takwas na ɗauke da Al´arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.
18; A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyħwa.
19; To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), “Ku karɓa, ku karanta littafina.”
20; “Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne.”
21; Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
22; A cikin Aljanna maɗaukakiya.
23; Nunannun ´yã´yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
24; (Ana ce musu) “Ku ci, kuma ku sha a cikin ni´ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige.”
25; Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: “Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!”
26; “Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!”
27; “In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
28; “Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!”
29; “Ĩkona ya ɓace mini!”
30; (Sai a ce wa malã´iku) “Ku kãmã shi, sa´an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi.”
31; “Sa´an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi.”
32; “Sa´an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã´i saba´in, sai ku sanya shi.”
33; “Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!”
34; “Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!”
35; “Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi.”
36; “Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn.”
37; “Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci.”
38; To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
39; Da abin da bã ku iya gani.
40; Lalle ne, shi (Alƙur´ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
41; Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
42; Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
43; Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
44; Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garħ Mu.
45; Dã Mun kãma shi da dãma.
46; sa´an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
47; Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
48; Kuma lalle ne shi (Alƙur´ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
49; Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cħwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
50; Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
51; Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshħni.
52; Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.

Pages ( 69 of 114 ): « Previous1 ... 6768 69 7071 ... 114Next »