Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 71 (Sura 71)
1; Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cħwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
2; Ya ce: “Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa.”
3; “Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni.”
4; “Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci).”
5; Nũhu) ya ce: “Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini.”
6; “To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni).”
7; “Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai.”
8; “Sa´an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane.”
9; “Sa´an nan lalle ne, na yi yħkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri.”
10; “Shi na ce, ´Ku nħmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.”
11; “Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.”
12; “Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya,Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna.”
13; “Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,”
14; “Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?”
15; “Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?”
16; “Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?”
17; “Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa.”
18; “Sa´an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa.”
19; “Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya.”
20; “Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi.”
21; Nũhu ya ce: “Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra.”
22; “Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba.”
23; “Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya´ũƙa da Nasra.”
24; “Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata.”
25; Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa´an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
26; Kuma Nũhu ya ce: “Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida.”
27; “Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci”
28; “Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka.”

Pages ( 71 of 114 ): « Previous1 ... 6970 71 7273 ... 114Next »