Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 1 (Sura 1)
1; Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
2; Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
3; Mai rahama, Mai jin ƙai;
4; Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
5; Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
6; Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
7; Hanyar waɗanda Ka yi wa ni´ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.

Pages ( 1 of 114 ): 1 23 ... 114Next »