Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 68 (Sura 68)
1; Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
2; Kai, sabõda ni´imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
3; Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
4; Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
5; Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
6; Ga wanenku haukã take.
7; Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
8; Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
9; Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
10; Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
11; Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
12; Mai hana alhħri mai zãlunci, mai zunubi.
13; Mai girman kai, bãyan haka kuma la´ĩmi ( bã ya son alhħri).
14; Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
15; Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: “Tatsũniyõyin mutãnen farko ne.”
16; Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
17; Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
18; Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgħwa.
19; Wani mai kħwayãwa daga Ubangijinka ya kħwayã a kanta, ( ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
20; Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
21; Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
22; Cħwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
23; Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cħwa).
24; “Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!”
25; Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
26; Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: “Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!”
27; “Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne.”
28; Mafificinsu (hankali) ya ce: “Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?”
29; Suka ce: “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai.”
30; Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
31; Suka ce: “Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙħtare iyãka.”
32; “Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne.”
33; Haka dai azãbar(1) take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnħwã.
34; Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni´ima.
35; Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa´a kamar mãsu laifi?
36; Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
37; Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
38; Cħwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
39; Kõ kunã ( riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar Ƙiyãma, cħwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
40; Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
41; Kõ sunã da abõkan tãrħwa (ga wannan ra´ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
42; Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba.
43; Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
44; Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur´ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
45; Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.
46; Kõ kana tambayar su wata la´ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
47; Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
48; Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma´abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
49; Ba dõmin ni´ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jħfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
50; Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa´an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
51; Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur´ãni, kuma sunã cħwa, “Lalle ne shi mahaukaci ne!”
52; Shi ( Alƙur´ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.

Pages ( 68 of 114 ): « Previous1 ... 6667 68 6970 ... 114Next »