Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 107 (Sura 107)
1; Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
2; To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa).
3; Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
4; To, bone yã tabbata ga masallata.
5; Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.
6; Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu)
7; Kuma suna hana taimako.

Pages ( 107 of 114 ): « Previous1 ... 105106 107 108109 ... 114Next »