Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 77 (Sura 77)
1; Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jħre, sunã bin jũna.
2; Sa´an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
3; Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
4; sa´an nan, da ãyõyi(1) mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabħwa.
5; Sa´an nan da malã´iku mãsu jħfa tunãtarwa ga Manzanni.
6; Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
7; Lalle ne, abin da ake yi muku wa´adi da shi tabbas mai aukuwa ne
8; To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
9; Kuma, idan sama aka tsãge ta.
10; Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
11; Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
12; Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
13; Domin rãnar rarrabħwa(2) .
14; Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabħwa?
15; Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
16; Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
17; Sa´an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
18; Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
19; Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
20; Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
21; Sa´an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
22; Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
23; Sa´an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
24; Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
25; Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
26; Ga rãyayyu da matattu,
27; Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
28; Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
29; Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
30; Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
31; Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
32; Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
33; Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
34; Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
35; Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
36; Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
37; Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
38; Wannan rãnar rarrabħwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
39; To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
40; Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
41; Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marħmari.
42; Da wasu ´ya´yan itãce irin waɗanda suke marmari.
43; (A ce musu) “Ku ci ku sha cikin ni´ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa.”
44; Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
45; Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
46; (Ana ce musu) “Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne.”
47; Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
48; Kuma, idan an ce musu: “Ku yi rukũ´i; bã zã su yi rukũ´in (salla) ba.”
49; Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
50; To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur´ãni) zã su yi ĩmãni

Pages ( 77 of 114 ): « Previous1 ... 7576 77 7879 ... 114Next »