Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 87 (Sura 87)
1; Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
2; Wanda Yã yi halitta sa´an nan Ya daidaita abin halittar.
3; Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar,(da mutum ga hanyar alhħri da ta sharri).
4; Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
5; Sa´an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
6; Za mu karantar da kai (Alƙur´ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
7; Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
8; Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al´amari) zuwa ga (Shari´a) mai sauƙi.
9; Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
10; Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
11; Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
12; Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
13; Sa´an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
14; Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
15; Kuma ya ambaci sũnan(5) Ubangijinsa, sa´an nan yã yi salla.
16; Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.(1)
17; Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
18; Lalle ne, wannan(2) yanã a cikin littafan farko.
19; Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.

Pages ( 87 of 114 ): « Previous1 ... 8586 87 8889 ... 114Next »