Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 81 (Sura 81)
1; Idan rãna aka shafe haskenta
2; Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
3; Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
4; Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna(1) aka sakħ su wãwai, bã ga kõwa ba.
5; Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
6; Kuma idan tħkuna aka mayar da su wuta.
7; Kuma idan rãyuka aka haɗa(2) su da jikunkunansu.
8; Kuma idan wadda aka turbuɗe(3) ta da rai aka tambaye ta.
9; “Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?”
10; Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
11; Kuma idan sama aka fħɗe ta.
12; Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
13; Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
14; Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
15; To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã(4) ba.
16; Mãsu gudu suna ɓũya.
17; Da dare idan ya bãyar da bãya.
18; Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
19; Lalle ne shi (Alƙur´ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
20; Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al´arshi.
21; Wanda ake yi wa ɗã´a (wato shugaban malã´iku) ne a can, amintacce.
22; Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
23; Kuma lalle ne, yã gan shi(5) a cikin sararin sama mabayyani.
24; Kuma shi, ga gaibi(6) bã mai rowa ba ne.
25; Kuma shi (Alƙur´ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la´ana, ba ce.
26; Shin, a inã zã ku tafi?
27; Lalle ne shi (Alƙur´ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
28; Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
29; Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.

Pages ( 81 of 114 ): « Previous1 ... 7980 81 8283 ... 114Next »