Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 15 (Sura 15)
1; A. L̃. R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.
2; Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.(1)
3; Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa´an nan da sannu zã su sani.
4; Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.
5; Wata al´umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.
6; Suka ce: “Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur´ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne.”
7; “Dõmin me bã zã ka zo mana da malã´ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?”
8; Bã Mu sassaukar da malã´iku fãce da gaskiya,(2) bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.
9; Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur´ãni), kuma lalle Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayħwane gare shi.
10; Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka.
11; Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.
12; Kamar wancan ne Muke shigar da shi(3) a cikin zukãtan mãsu laifi.
13; Bã su yin ĩmãni da shi,(4) kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.
14; Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.
15; Lalle ne dã sun ce: “Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. ôa, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce.”
16; Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
17; Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
18; Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.
19; Kuma ƙasa Mun mĩkħ ta kuma Mun jħfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikħli.
20; Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã(1) da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
21; Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.
22; Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa´an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacħwa a gare shi ba.
23; Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashħwa kuma Mũ ne magada.
24; Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.
25; Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
26; Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.
27; Kuma Aljani Mun haliccħ shi daga gabãni, daga wutar (2) iskar zafi.
28; Kuma a l?kacin da Ubangijinka ya ce wa mal?´iku: “Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙeƙasasshen yumɓu wanda ya canja.”
29; “To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa(3) a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada.”
30; Sai malã´iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
31; Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancħwa daga mãsu yin sujadar.
32; Ya ce: “Yã Iblĩs mħne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?”
33; Ya ce: “Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja.”
34; Ya ce: “To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne.”
35; “Kuma lalle ne akwai la´ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako.”
36; Ya ce: “Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su.”
37; Ya ce: “To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri.”
38; “Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne.”
39; Ya ce: “Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya.”
40; “Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake.”
41; Ya ce: “Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici.”
42; “Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu.”
43; Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma´alkawartarsu gabã ɗaya.
44; Tanã da ƙõfõfi bakwai,(1) ga kõwace ƙõfa akwai wani juz´i daga gare su rababbe.
45; Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.
46; “Ku shigħ ta da aminci, kunã amintattu.”
47; Kuma Muka ɗħbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama ´yan´uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.
48; Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga cikinta ba.
49; Ka bai wa bãyiNa lãbari cħwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.
50; Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.
51; Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.
52; A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: “Sallama.” Ya ce: “Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne.”
53; Suka ce: “Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi maka bushãra game da wani yãro masani.”
54; Ya ce: “Shin kun bã ni bushãra(1) ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?”
55; Suka ce: “Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni.”
56; Ya ce: “Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?”
57; Ya ce: “To, mħne ne babban al´amarinku? Yã kũ manzanni!”
58; Suka ce: “Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi.”
59; “Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya.”
60; “Fãce mãtarsa mun ƙaddara cħwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka.”
61; To, a lõkacin da mazannin suka jħ wa mutãnen Lũɗu,
62; Ya ce: “Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba.”
63; Suka ce: “ôa, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa.”
64; “Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne.”
65; “Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka umurce ku.”
66; Kuma Muka hukunta wancan al´amarin zuwa gare shi cħwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankħwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba.
67; Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
68; Ya ce: “Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni.”
69; “Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki.”
70; Suka ce: “Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?”
71; Ya ce: “Ga waɗannan ´ya´yãna (1) idan kun kasance mãsu aikatãwa ne.”
72; Rantsuwa da(2) rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
73; Sa´an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
74; Sa´an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
75; Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
76; Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a għfen wata hanyã tabbatacciya.(3)
77; Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
78; Kuma lalle ne ma´abũta Al´aika(4) sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
79; Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a għfen wani tafarki mabayyani.
80; Kuma lalle ne haƙĩƙa ma´abũta Hijiri(5) sun ƙaryata Manzanni.
81; Kuma Muka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirħwa daga gare su.
82; Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
83; Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba.
84; Sa´an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
85; Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã´a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
86; Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
87; Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu(6) da Alƙur´ãni mai girma.
88; Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau´i-nau´i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
89; Kuma ka ce: “Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne.”
90; Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,(7)
91; Waɗanda suka sanya Alƙur´ãni tãtsuniyõyi.
92; To, rantsuwa da Ubangijinka! (1) Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.
93; Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
94; Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.
95; Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu(2) izgili.
96; Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa´an nan da sannu zã su sani.
97; Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cħwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).
98; Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.
99; Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.

Pages ( 15 of 114 ): « Previous1 ... 1314 15 1617 ... 114Next »