Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 90 (Sura 90)
1; Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari (1) ba.
2; Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
3; Da mahaifi da abin da ya haifa.
4; Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
5; Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
6; Yana cħwa “Na(2) halakarda dũkiya mai yawa,”
7; Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
8; Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
9; Da harshe, da leɓɓa biyu.
10; Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi(3) biyu ba?
11; To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
12; Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cħ wa Aƙabã?
13; Ita ce fansar wuyan bãwa.
14; Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma´abũcin yunwa.
15; Ga marãya ma´abũcin zumunta.
16; Ko kuwa wani matalauci ma´abũcin turɓãya.
17; Sa´an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
18; Waɗannan ne ma´abũta albarka(4)
19; Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma´abũta shu´umci(5)
20; A kansu akwai wata wuta abar kullewa.

Pages ( 90 of 114 ): « Previous1 ... 8889 90 9192 ... 114Next »