Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 101 (Sura 101)
1; Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
2; Mħnħ ne mai ƙwanƙwasa?
3; Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
4; Rãnar da mutãne za su kasance kamar ´ya´yan fari mãsu wãtsuwa.
5; Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
6; To, amma wanda ma´aunansa suka yi nauyi.
7; To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
8; Kuma amma wanda ma´aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
9; To, uwarsa Hãwiya ce.
10; Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
11; Wata wuta ce mai zafi.

Pages ( 101 of 114 ): « Previous1 ... 99100 101 102103 ... 114Next »