Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 97 (Sura 97)
1; Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur´ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
2; To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Ƙadari?
3; Lailatul Ƙadari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
4; Mala´iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
5; Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.

Pages ( 97 of 114 ): « Previous1 ... 9596 97 9899 ... 114Next »