Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 55 (Sura 55)
1; (Allah) Mai rahama.
2; Yã sanar da Alƙur´ani.
3; Yã halitta mutum.
4; Yã sanar da shi bayãni (magana).
5; Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
6; Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu´i.
7; Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikħli.
8; Dõmin kada ku karkatar da sikħlin.
9; Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikħlin.
10; Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
11; A cikinta akwai ´ya´yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
12; Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
13; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangjinku(1) kuke ƙaryatãwa?
14; Yã halitta mutum daga ƙħkasasshen yumɓu kumar kasko.
15; Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
16; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
17; Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
18; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
19; Yã garwaya tħku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.
20; A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
21; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
22; Lu´ulu´u da murjãni na fita daga gare su.
23; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
24; Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tħku kamar manyan duwãtsu.
25; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
26; Dukkan wanda ke kanta(1) mai ƙãrħwa ne.
27; Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
28; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
29; wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha´ani.
30; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
31; Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ(2) mãsu nauyin halitta biyu!
32; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
33; Ya jama´ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcħwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcħwaba fãce da wani dalĩli.
34; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
35; Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nħmi taimako ba?
36; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
37; Sa´an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
38; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
39; To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.
40; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
41; zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
42; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
43; Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
44; Sunã kħwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
45; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
46; Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
47; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
48; Mãsu rassan itãce.
49; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
50; A cikinsu akwai marħmari biyu sunã gudãna.
51; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
52; A cikinsu akwai nau´i biyu daga kõwane ´ya´yan itãcen marmari.
53; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
54; Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun ´yã´yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.
55; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
56; A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
57; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
58; Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
59; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
60; Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (ôaha) fãce kyautatãwa.
61; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
62; Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
63; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
64; Mãsu duhun inuwa.
65; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
66; A cikinsu akwai marħmari biyu masu kwarãrar ruwa.
67; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
68; A cikinsu akwai ´ya´yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
69; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
70; A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
71; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
72; Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
73; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
74; Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗħbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
75; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
76; Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
77; To, sabõda wanne daga ni´imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
78; Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.

Pages ( 55 of 114 ): « Previous1 ... 5354 55 5657 ... 114Next »