Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 51 (Sura 51)
1; Inã rantsuwa da iskõki mãsu shħkar abũbuwa, shħƙħwa.
2; Sa´an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
3; Sa´an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
4; Sa´an nan da Malã´iku mãsu rabon al´amari (bisa umurnin Allah).
5; Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
6; Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
7; Inã rantsuwa da samã ma´abũciyar hanyõyi ( na tafiyar taurãri da sautin rediyo).
8; Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur´ani).
9; Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
10; An la´ani mãsu ƙiri-faɗi.
11; Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
12; Sunã tambaya: “Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?”
13; Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.
14; (A ce musu): “Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nħman zuwansa da gaggãwa.”
15; Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marħmari.
16; Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).
17; Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
18; Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
19; Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
20; Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
21; Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?
22; Kuma a cikin sama arzikinku ( yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.
23; To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
24; Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
25; A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce “Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!”
26; Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa´an nan ya zo da maraƙi tutturna,
27; Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: “Bã zã ku ci ba?”
28; Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: “Kada kaji tsõro.” Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.
29; Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: “Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!”
30; Suka ce: “Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi.”
31; (Ibrãĩm) ya ce: “To mħne ne babban al´almarinku, yã kũ Manzanni!”
32; Suka ce: “Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
33; “Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu ( bom).
34; “Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna.”
35; Sa´an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
36; Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
37; Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
38; Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir´auna da wani dalĩli bayyananne.
39; Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: “Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci !”
40; Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa´an nan Muka jħfa su a cikin tħku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
41; Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙħƙasasshiya a kansu.
42; Bã ta barin kõme da ta jħ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
43; Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: “Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,”
44; Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
45; Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nħman ãgaji ba.
46; Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
47; Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
48; Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
49; Kuma daga kõme Mun halitta nau´i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
50; Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
51; Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
52; Kamar haka dai wani Manzo bai jħ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: “Mai sihiri ne kõ mahaukaci.”
53; shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? ôa, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
54; Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
55; Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
56; Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
57; Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.(1)
58; Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
59; To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
60; Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.

Pages ( 51 of 114 ): « Previous1 ... 4950 51 5253 ... 114Next »