Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 92 (Sura 92)
1; Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufħwa.
2; Da yini a lõkacin da yake kuranyħwa.
3; Da abin da ya halitta namiji da mace.
4; Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
5; To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
6; Kuma ya gaskata kalma(3) mai kyãwo.
7; To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
8; Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
9; Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
10; To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
11; Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
12; Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
13; Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
14; Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
15; Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
16; Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
17; Kuma mafi taƙawa(1) zai nisance ta.
18; Wanda yake bãyar da dũkiyarsa ,alhãli yana tsarkaka.
19; Alhãli bãbu wani mai wata ni´ima wurinsa wadda ake nħman sakamakonta.
20; Fãce dai nħman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
21; To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi) .

Pages ( 92 of 114 ): « Previous1 ... 9091 92 9394 ... 114Next »