Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 94 (Sura 94)
1; Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
2; Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
3; Wanda ya nauyayi bãyanka?
4; Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
5; To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
6; Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
7; Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
8; Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.

Pages ( 94 of 114 ): « Previous1 ... 9293 94 9596 ... 114Next »