Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 84 (Sura 84)
1; Idan sama ta kħce,
2; Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
3; Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
4; Kuma ta jħfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
5; Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
6; Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
7; To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
8; To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
9; Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
10; Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
11; To, zã shi dinga kiran halaka!
12; Kuma ya shiga sa´ĩr.
13; Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
14; Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
15; Na´am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
16; To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
17; Da dare, da abin da ya ƙunsa.
18; Da watã idan (haskensa) ya cika.
19; Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
20; To, mħ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
21; Kuma idan an karanta Alkur´ãni a kansu, bã su yin tawãli´u?
22; Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
23; Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
24; Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
25; Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankħwa.

Pages ( 84 of 114 ): « Previous1 ... 8283 84 8586 ... 114Next »