Chapter 66 (Sura 66)
1; Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka,(1) kanã nħman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
2; Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware(2) rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.
3; Kuma a sã´ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: “Wãne ne ya gaya maka wannan?” Ya ce: “Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini.”
4; Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã´iku a bãyan wancan, mataimaka ne.
5; Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure mafiya alhħri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli´u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da ´yammãta.
6; Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku(3) (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã´iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su.
7; Yã kũ waɗanda suka kãfirta(4) ! Kada ku kãwo wani uzuri a yau. Anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa kawai ne.
8; Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi(1) da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cħwa, “Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne.”
9; Yã kai Annabi! Ka yãki kãfirai da munãfwkai. Kuma ka tsananta a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce, kuma tir da makoma, ita.
10; Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta(2) : mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyinMu sãlihai, saisuka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: “Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga.”
11; Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir´auna,(3) sa´ad da ta ce “Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir´auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai.”
12; Da Maryama(4) ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da LittattafanSa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli´u.
Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani
Pages: 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114