Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 70 (Sura 70)
1; Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
2; Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗħwa.
3; Daga Allah Mai matãkala.
4; Malã´iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shħkara dubu hamsin ne.
5; Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
6; Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
7; Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
8; Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
9; Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
10; Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
11; Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
12; Da matarsa da ɗan´uwansa.
13; Da danginsa, mãsu tattarã shi.
14; Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa´an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
15; A´aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
16; Mai twãle fãtar goshi.
17; Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
18; Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
19; Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
20; Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
21; Kuma idan alhħri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
22; Sai mãsu yin salla,
23; Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
24; Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
25; Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
26; Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
27; Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
28; Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincħwaba ce.
29; Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
30; Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
31; To, duk wanda ya nħmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
32; Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarħwa ne.
33; Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgħwa ne.
34; Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarħwa ne.
35; Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
36; Mħ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
37; Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama´a-jama´a!
38; Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nħman a shigar da shi a Aljannar ni´ima ne (ba da wani aiki ba)?
39; A´aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
40; Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
41; Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhħri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
42; Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita) .
43; Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
44; Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)

Pages ( 70 of 114 ): « Previous1 ... 6869 70 7172 ... 114Next »