Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 91 (Sura 91)
1; Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
2; Kuma da wata idan ya bi ta.
3; Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
4; Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
5; Da sama da abin da ya gina ta.
6; Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
7; Da rai da abin da ya daidaita shi.
8; Sa´an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
9; Lalle ne wanda ya tsarkake(1) shi (rai) ya sãmi babban rabo.
10; Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe(2) shi (da laifi) ya tãɓe.
11; Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
12; A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
13; Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: “Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!”
14; Sai suka ƙaryata shi, sa´an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa´an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
15; Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

Pages ( 91 of 114 ): « Previous1 ... 8990 91 9293 ... 114Next »