Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 96 (Sura 96)
1; Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
2; Ya hahitta mutum daga gudan jini.
3; Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
4; Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
5; Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
6; A´aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
7; Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
8; Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
9; Shin, kã ga wanda ke hana.
10; Bãwã idan yã yi salla?
11; Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
12; Ko ya yi umurni da taƙawa?
13; Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
14; Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
15; A´aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
16; Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
17; Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
18; Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala´iku mãsu girma).
19; A´aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali´u,(5) kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).

Pages ( 96 of 114 ): « Previous1 ... 9495 96 9798 ... 114Next »