Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 75 (Sura 75)
1; Bã sai Nã yi rantsuwa(1) da Rãnar Ƙiyãma ba.
2; Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin(2) kansa ba.
3; Sin, mutum yana zaton cħwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
4; Na´am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
5; Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
6; Yanã tambaya: “Yaushe ne Rãnar Ƙiyãma?”
7; To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
8; Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
9; Aka tãra rãnã da watã
10; Mutum zai ce a rãn nan “Ina wurin gudu?”
11; A´aha! bãbu mafaka.
12; zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
13; Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
14; Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
15; Kuma ko da yã jħfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
16; Kada ka mõtsar(3) da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur´ãni).
17; Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
18; To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
19; sa´an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
20; A´aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
21; Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
22; Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
23; Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
24; Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsħwa ne.
25; Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
26; A´aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
27; kuma aka ce: “Wãne ne mai tawada?”
28; Kuma ya tabbata cħwa rabuwa dai ce.
29; Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
30; Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa(1) take.
31; To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
32; Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
33; Sa´an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
34; Halaka tã tabbata a gare ka, sa´an nan ita ce mafi dãcewa.
35; Sa´an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
36; Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi) ?
37; Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa( a cikin mahaifa)
38; Sa´an nan, ya zama gudan jini, sa´an nan Allah Ya halitta shi, sa´an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
39; Sa´an nan, Ya sanya daga gare shi, nau´i biyu: namiji damace?
40; Ashħ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?(2)

Pages ( 75 of 114 ): « Previous1 ... 7374 75 7677 ... 114Next »