Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 93 (Sura 93)
1; Inã rantsuwa da hantsi.
2; Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
3; Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
4; Kuma lalle ta ƙarshe(2) ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
5; Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
6; Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa´an nan Ya yi maka makõma?
7; Kuma Ya sãme ka bã ka da shari´ã, sai Ya shiryar da kai?
8; Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
9; Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
10; Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
11; Kuma amma ni´imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).

Pages ( 93 of 114 ): « Previous1 ... 9192 93 9495 ... 114Next »