Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 85 (Sura 85)
1; Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
2; Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,(1)
3; Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta(2) a cikinsa
4; An la´ani mutãnen rãmi.(3)
5; Wato wuta wadda aka hura.
6; A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
7; Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
8; Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
9; Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
10; Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa´an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
11; Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
12; Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
13; Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
14; Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
15; Mai Al´arshi mai girma
16; Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
17; Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
18; Fir´auna da samũdãwa?
19; ôaha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
20; Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kħwaye su ne (da saninSa).
21; ôaha! Shi Alƙur´ãni ne mai girma.
22; A cikin Allo tsararre.

Pages ( 85 of 114 ): « Previous1 ... 8384 85 8687 ... 114Next »