Hausa Quran | Karanta Al-Qur’ani

Chapter 95 (Sura 95)
1; Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.(1)
2; Da Dũr Sĩnĩna(2) .
3; Da wannan gari(3) amintacce.
4; Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
5; Sa´an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
6; Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
7; To, bãyan haka mħ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin Ƙiyãma)?
8; Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?(4)

Pages ( 95 of 114 ): « Previous1 ... 9394 95 9697 ... 114Next »